Isa ga babban shafi
Amurka

Trump ya kori shugaban hukumar leken asiri James Comey

Shugaban Amurka Donald Trump ya kori shugaban hukumar leken asirin kasar James Comey wanda ke jagorancin binciken da ake yiwa jami’an sa na hadin kai da wasu jami’an Rasha dan sauya sakamakon zaben kasar.

Trump ya kori shugaban hukumar leken asirin kasar Amurka James Comey
Trump ya kori shugaban hukumar leken asirin kasar Amurka James Comey REUTERS/Kevin Lamarque
Talla

A wani yanayin fargaba da ake alakanta shi da badakalar Watergate wadda tayi awon gaba da kujerar tsohon shugaban Amurka, Richard Nixon, Donald Trump ya shaidawa James Comey cewar Hukumar ta FBI na bukatar sabon shugaba saboda haka ya dakatar da shi daga aiki.

A karkashin jagorancin Comey, Hukumar FBI ta bayyana cewar shugaban Rasha Vladimir Putin ya taka rawa wajen sauya alkiblar zaben Amurka dan taimakawa shugaba Trump.

Korar Comey wanda ke zuwa bayan na Sally Yates Babbar Lauyan Gwamnati, ya gamu da suka daga Yan Jam’iyyar Democrat da suke zargin cewar ana neman rufa rufa ne akan bincike binciken da yake jagoranci.

A tarihin Hukumar ta FBI, shugaba guda aka taba kora, kafin Comey wanda Donald Trump ya kora.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.