Isa ga babban shafi
Amurka

FBI na binciken alakar Trump da Rasha

Shugaban Hukumar tsaron FBI ta Amurka James Comey ya tabbatar da cewa hukumarsa na binciken alakar yakin neman zaben Donald Trump da Rasha tare da yin watsi da zargin sauraron bayanan shugaba Donald Trump da ake yi wa tsohon shugaban kasa Barack Obama.

Shugaban Hukumar bincike ta FBI a Amurka James Comey
Shugaban Hukumar bincike ta FBI a Amurka James Comey REUTERS/Joshua Roberts
Talla

Comey ya bayyana haka ne lokacin da ya ke bayani a gaban wani kwamitin Majalisar wakilai da aka watsa kai tsaye a kafofin yada labaran Amurka.

Ya tabbatar da cewa FBI na gudanar da binciken kan zargin ko Trump ya yi alaka da Rasha da nufin karya abokan hammayarsa a zaben 2016.

Sai dai shugaban na FBI ya ki amsa tambayoyi kan aininin wadanda bincikensu ya shafa da kuma abinda suke bincike akai domin tabbatar da ko Trump ya yi alaka da Rasha.

Amurka na zargin Rasha da yin katsalandan ga sha’anin zabenta domin taimakawa Trump na Republican lashe zaben kasar da aka gudanar a watan Nuwamba.

Jam’iyyar Democrats da ta sha kaye a zaben ta zargi Rasha da yin kutse a shafin kamfen na ‘yar takarar Jam’iyyar Hillary Clinton.

Amma tun lokacin shugaba Donald Trump ke musanta zargin.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.