Isa ga babban shafi
Rasha

An yi gagarumin kutse a bankunan Rasha

An kaddamar da wani gagarumin kutse ta shafukan intanet na wasu manyan bankunan kasar Rasha guda biyar kamar yadda kamfanin Kaspersky mai tsaron shafukan Intanet ya sanar.

An yi amfani da kwamfutoci dubu 24 wajen yin kutsen a bankunan Rasha
An yi amfani da kwamfutoci dubu 24 wajen yin kutsen a bankunan Rasha Reuters/路透社
Talla

Kaspersky ya ce, tun a ranar Talatar da ta wuce aka kaddamar da kutsen a manyan bankuna biyar daga cikin 10 da ake ji da su a Rashan.

Bankin Sberbank da ke karkashin kulawar gwamnatin kasar ya tabbatar da kutsen a bangarensa, duk da dai daga bisani ya yi nasarar dakile kutsen.

Ko a jiya sai da masu kutsen suka ci gaba da aikin nasu, in da akasarinsu suka shafe akalla sa’a guda wajen yin kutsen yayin da wasunsu suka shafe kusan sa’oi 12.

Kutsen dai ya haddasa gagarumin cinkoso a shafukan na intanet, matsalar da ke da wuyar magance wa cikin lokaci ga bankunan.

An dai yi amfani da kwamfutoci har guda dubu 24 masu zaman kasnu daga kasashe 31 da suka hada da Amurka da India da Taiwan da Isra’ila wajen kai wannan gagarumin farmakin.

Hukumomin bankunan sun ce, matsalar dai ba ta shafi huldarsu da kwastamominsu ba musamman wadanda ke mu’amala da su ta intanet.

A karon farko kenan da aka yi irin wannan kusten a bankunan Rasha a cikin wannan shekarar. Amma a cikin watan Octoban bara sai da aka kai irin wannan kutsen a bankuna 8 na kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.