Isa ga babban shafi
Bakin-Haure-Turai

Bakin haure 700 sun nutse a Teku Baharum

Majalisar Dinkin Duniya ta ce akalla bakin haure 700 sun rasa rayukansu a kasa da mako guda, bayan nutsewar da kanana jiragen dake dauke da su ya yi a tekun Bahar Rum.

Hotuna Jirgin da ya kefe da bakin haure a Tekun Baharrum
Hotuna Jirgin da ya kefe da bakin haure a Tekun Baharrum STR / AFP MARINA MILITARE / AFP
Talla

Wadanda aka ceto daga Tekun na Baharrum zuwa tashar jirgin Taranto da Pozzallo na Italiya, sun shaidawa hukumar ‘yan gudun hijira ta MDD yadda jirgin da suke ciki ya nitse bayan gamu wa da matsala.

A cewar Carlotta Sami, Jami’a a hukumar, mutane da aka ceto sun gaggara tanttace adaddin mutane da suka mutu, ko fayyace  kasashen su, sai dai sun tabbatar da cewa mutane da jirgin ya nitse dasu sun kai 500.

Da alkallumar dake tabbatar da bacewar wasu bakin haure na daban 100, a tekun ranar laraba da ta gabata, da kuma tsinto gawarwaki 45 a tekun ranar Juma’a, hukumar ta kiyasta cewa akalla mutane 700 ne suka rasa rayukansu a kokarinsu na shiga turai a makon daya gabata.

Giovanna Di Benedetto, mai magana da yawun kungiyar Save the Chidren, ta shaidawa kamfanin dilanci labaran faransa AFP cewa, wadanda suka tsira da ransu a ranar alhamis, sunce kusan mutane 1,100 ne suka taso a kanana jirage daga Libya ranar Laraba da nufin shiga turai, kafin su hadu da matsalar da tayi sanadi kefewar jirgin.

Giovanna ta ce, mutane da dama sun fada cikin ruwan lokacin da suka ankara jirgin da suke ciki ya fara nitsewa.

A yanzu dai ana tsare da direben daya daga cikin jiragen dan asalin Sudan da wasu mutane 3 da ake zargi da fataucin bakin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.