Isa ga babban shafi
mdd- Girka

MDD ta bukaci Girka ta kyautata wa baki

Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira ga Girka ta inganta rayuwar dubban 'yan gudun hijira yawancinsu kananan yara wadanda ke jiran tsammanin samun mafaka a kasar karkashin tsarin yarjejeniyar nan ta ‘yan gudun hijirar mai tsauri da Tarayyar Turai ta kulla da Turkiya.

'Yan gudun hijira a tsibirin Lesbos na Girka
'Yan gudun hijira a tsibirin Lesbos na Girka REUTERS/Giorgos Moutafis
Talla

Ofishin kare hakkin bil’adama na Majalisar bayyana damuwar ne kan matsaloli na rashin samun bayanai da suka shafi ‘yan gudun hijirar da kuma yadda aka gwamatsa su a sansanin da Girka ta tanar ma su.

A cikin wata sanarwa, babban jami’in hukumar ya yi kira ga Girka ta canja salon tsare ‘yan gudun hijirar har zuwa lokacin da za su samu shedar izinin tsallakawa zuwa Turai.

Girka dai ta tsaurara matakai ne akan ‘yan gudun hijirar karkashin tsarin yarjejeniyar da Tarayyar Turai ta amince da Turkiya, ta maido da 'yan gudun hijirar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.