Isa ga babban shafi
Turai

Kasashen Turai na taro kan 'yan gudun hijira

Shugabannin Kungiyar kasashen Turai za su gudanar da wani taro na kwanaki biyu daga yau a birnin Rome don nazarin halin da ake ciki kan matsalar baki.

Bakin na ci gaba da kwarara zuwa Turai
Bakin na ci gaba da kwarara zuwa Turai 路透社
Talla

Firaministan Italiya Matteo Renzi ke daukan nauyin taron na yau yayin da yake tsoron kada kasarsa ta zama sansanin baki, ganin cewar yanzu haka dubu 28 da 500 sun isa kasar a cikin watanni hudu da suka gabata.

Shugabanin za su yi kokarin ganin sun samu masalaha kan matsalar da ke kara girma kafin mayar da hankalinsu kan shirin gudanar da kuri’ar raba gardama kan makomar Birtaniya a kungiyar da kuma rikicin bashin kasar Girka.

Cikin wadanda ake sa ran za su halarci taron har da shugaban kungiyar kasashen Turai Donald Tusk da shugaban hukumar Turai Jean Claude Juncker da shugaban majalisar Turai Martin Schulz.

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.