Bakonmu a Yau
A kullum mukan gayyaci masana a fannoni daban daban domin tattauna wasu muhimman al'amurra da suka shafi kanun labarai a duniya. wani lokacin kuma wasu manyan jami'an gwamnati da masu fada aji sukan kawo muna ziyara domin tattauna batutuwan da suka shafi matsalolin da suka shafe su ko kuma ci gaban kasa.
Ci gaban karatuSaurari kashin karshe
Daukacin kashi-kashi
-
Nuhu Abayo Toro: Kan Ranar Ma'aikata ta Duniya
Yau ce ranar Ma’aikata ta Duniya, kuma bikin na wannan shekara na zuwa ne a cikin mawuyacin hali ga ma’aikatan Najeriya, sakamakon koma bayan tattalin arzikin kasar da kuma kuncin rayuwar da suka samu Kansu.Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Nuhu Abbayo Toro, Sakatare Janar na kungiyar kwadago ta kasa ta TUC.01/05/202403:23 -
Dr. Kasim Kurfi: Kan rashin tsayuwar karfin naira
Bayan yin bazata wajen farfaɗowa daga faɗuwar da yayi a watannin baya, kuɗin Najeriya ya fuskanci koma baya musamman a makon jiya, inda a kasuwar canjin bayan fage aka sayar da dala guda kan Naira 1,400.01/05/202402:59 -
Tattaunawa da Nuhu Abbayo Toro na TUC kan ranar ma'aikata a Najeriya
Yau ake bikin ranar ma’aikata ta Duniya, wadda a bana ke zuwa a lokacin da ake fuskantar ƙarin matsalolin da a wasu sassa ko kasashe za iya cewa ruɓanyawa suka yi, musamman ma ƙalubalen matsin tattalin arziƙi.01/05/202403:23 -
Dr Kasim Kurfi kan yadda darajar nairar Najeriya ke kwan-gaba kwan-baya
Bayan yin bazata wajen farfaɗowa daga faɗuwar da yayi a watannin baya, kuɗin Najeriya ya fuskanci koma baya musamman a makon jiya, inda a kasuwar canjin bayan fage aka sayar da dala guda kan Naira 1,400.01/05/202402:59 -
Tattaunawa da Bashir Ɗan Malam kan tsadar farashin mai a arewacin Najeriya
Harkokin kasuwanci da dama sun durkushe musamman a yankin arewacin Najeriya sakamakon tsadar farashin man fetur, inda ake sayar da lita guda a kan naira 2,000 zuwa 2,500 a kasuwar bayan-fage a jihar Sokoto. Kodayake akwai sassaucin farashin man a yankin kudancin kasar.29/04/202403:27 -
Munyi mamakin yadda Amurka ta san bayanan sirrin tsaron mu - Raɗɗa
Wasu gwamnonin arewacin Najeriya 10 da ke fuskantar matsalolin tsaro, sun kammala taron da suka je Amurka kan matsalar da kuma hanyoyin samar da zaman lafiya.26/04/202405:17 -
Bashir Dan-Malam kan karancin man fetur a sassan Najeriya
Rahotanni daga sassan arewacin Najeriya na nuna cewar an fara samun karancin mai a gidajen mai, abinda ya sa wasu masu man suka kara farashin da suke sayar da kowacce lita.25/04/202403:16 -
Alhaji Shehu Ashaka kan samar da 'yan sandan jihohi a Najeriya
Mahawara na ci gaba da zafi a Najeriya, dangane da yunkurin kirkiro ‘yan sandan jihohi domin taimakawa wajen inganta tsaron lafiya da dukiyoyin jama’a. Yayin da wasu jama’a ciki harda gwamnonin jihohi da tsoffin shugabannin kasa ke cewa lokaci ya yi da za a samar da ‘yan sandan, wasu kuma ciki harda Sufeto Janar na ‘yan sandan kasar na cewa har yanzu lokaci bai yi ba, saboda gwamnoni na iya amfani da su wajen biyan bukatun kan su.24/04/202403:14 -
Arewacin Najeriya aka fi kashe mutane a zangon farko na wannan shekarar - Rahoto
Wani bincike da kamfanin Beacon Securities ya yi a Najeriya, ya ce a watanni 3 na farkon wannan shekarar an kashe mutane sama da 2,500, yayin da aka yi garkuwa da wasu sama da dubu 2. Rahotan ya ce kashi 80 na wannan aika aika ana samun sa ne a yankin Arewacin Najeriya. Dangane da haka Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Air Commodore Tijjani Baba Gamawa mai ritaya.23/04/202403:19 -
Farfesa Mansur Isa Yelwa kan tsarin almajiranci a Najeriya
A karshen makon da ya gabata ne zabtarewar kasa ta hallaka wasu almajirai guda 8 a Jihar Kebbi, matsalar da ta dada tado da batun kula da almajiran da ke karatun Alkur'ani. Wasu na danganta matsalar da sakacin iyaye wajen rashin kula da 'ya'yan su ko kuma ciyar da su a makarantun allon.22/04/202403:33 -
Arewa maso Yammacin Najeriya ne mafi hatsari saboda matsalar tsaro - Bincike
Kungiyar 'Global Rights' ta bayyana yankin arewa maso yammacin Najeriya a matsayin mafi hadari, saboda yadda 'yan bindiga ke kisa da take hakkin Bil Adama ba tare da kaukautawa ba.18/04/202403:16 -
Kuskure ne a yi tunanin ɗagawar darajar naira ba zai ɗore ba - Dakta Kurfi
Darajar Naira na cigaba da ɗagawa a Najeriya tare da saukar farashin wasu kayayyakin abinci a wasu kasuwannin ƙasar, abinda ya sa wasu tunanin cewar tasirin saukar Dalar ne ya sanya wasu kayayyakin suka fara sauka.17/04/202403:19 -
Tattaunawa da Sanata Ikira Aliyu Bilbis kan tsaro a jihar Zamfara
Hukumomi a Najeriya daga matakin jiha zuwa na kasar baki ɗaya na daukar matakai daban daban wajen samar da zaman lafiya a jihar Zamfara, amma har ya zuwa wannan lokaci ba'a kai ga cimma biyan bukata ba.16/04/202403:26 -
Yadda rayuwa ta kasance bayan da muka faɗa hannun mayakan Boko Haram - Maryama
A ranar Lahadi, 14 ga watan Afrilun nan aka cika shekaru 10 da sace dalibai mata na makarantar sakandaren Chibok sama da 250 da mayakan Boko Haram suka yi a jihar Borno.15/04/202403:17 -
Kwamred Bello Basi kan shirin gina hanyayoin zamani a Najeriya
Gwamnatin Najeriya ta sanar da kashe naira biliyan 4 kan kowacce kilomita ta hanyar zamani da ake ginawa daga jihar Legas zuwa birnin Kalaba.12/04/202403:40
Bakonmu a Yau
A kullum mukan gayyaci masana a fannoni daban daban domin tattauna wasu muhimman al'amurra da suka shafi kanun labarai a duniya. wani lokacin kuma wasu manyan jami'an gwamnati da masu fada aji sukan kawo muna ziyara domin tattauna batutuwan da suka shafi matsalolin da suka shafe su ko kuma ci gaban kasa.