Isa ga babban shafi
Najeriya-Boko Haram

Sojin Najeriya sun dakile harin Boko Haram kan sansanin 'yan gudun hijira

Rundunar sojin Najeriya ta samu nasarar dakile wani hari da mayakan kungiyar boko haram suka shirya kaiwa kan sansanin ‘yan gudun hijira na Rann da ke jihar Borno.

Sansanin 'yan gudun hijira na Rann da ke Borno da mayakan Boko Haram sukai yunkurin kai hari
Sansanin 'yan gudun hijira na Rann da ke Borno da mayakan Boko Haram sukai yunkurin kai hari Médecins sans Frontières (MSF) / AFP
Talla

Lamarin na zuwa Sama da awanni 48 bayan kuskuren harin da jirgin yakin Najeriya ya kai kan sansanin wanda yayi sanadin kashe mutane akalla 90 ciki harda jami’an lafiya.

Rahotanni sun ce akalla mayakan guda 100 ne suka yi yunkurin tarwatsa sansanin amma sojin Najeriya suka maida musu martani, inda sukai nasarar kashe 5 daga cikin mayakan na Boko Haram tare da kwace mota kirar Hilux .

A cewar kwamandan da ke lura da bataliya ta 3 ta rundunar sojin Najeriya, Laftanar Kanal Patrick Omoke, sun shafe kimanin awanni hudu suna musayar wuta da mayakan, kafin su samu nasarar fatattakarsu.

A cewar Laftanar Kanal Omoke, wasu daga cikin mayakan na Boko Haram da suka hallaka, na rataye da bama bamai, da suka yi niyyar tayarwa idan har suka kutsa cikin sansanin yan gudun hijrar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.