Isa ga babban shafi
Najeriya

An kama jami'an da suka yi wa mata fyade a Borno

Hukumomin Najeriya sun kama jami’an tsaro da ake zargi da yi wa mata ‘yan gudun hijira fyade ko kuma lalata da su a sansanonin jihar Borno da ke yankin arewa maso gabashin kasar.

Daya daga cikin sansanin 'yan gudun hijira da ke jihar Borno ta Najeriya
Daya daga cikin sansanin 'yan gudun hijira da ke jihar Borno ta Najeriya STRINGER / AFP
Talla

Babban Supeta Janar na ‘yan sandan Najeriya, Ibrahim Idris ya bayyana cewa, an kama sojoji uku da jami’in kula da gidan kaso guda da kuma sojin sama guda, sai wani jami’i da ke aiki a ma’aikatar noma ta jihar Borno da kuma ‘yan kato da gora guda biyu.

Ana zargin mutanen da cin zarafin matan a sansanin da suke neman mafaka saboda rikicin Boko Haram da ya tilasta musu kaurace wa gidajensu.

Shugaban kasar ne Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin gudanar da bincike bayan kungiyar kare hakkin dan Adam ta Human Right Watch ta fitar da wani rahoto a cikin watan Oktoba, in da ta fallasa cin zarafin da jami’an suka yi wa matan.

Rahoton kungiyar ya ce, kimanin mata 43 aka ci zarafinsu a sansanoni guda bakwai da ke birnin Maiduguri.

Kungiyar ta kara da cewa, jami’an sun yi mata hudu fyade ne, yayin da kuma suka yaudari 37 har suka kwanta da su, bayan sun yi musu alkawura na kudade da aure.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.