Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari ya zargi Kungiyoyin agaji da wuce gona da iri

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya zargi kungiyoyin agaji na ciki da kuma kasashen ketare da wuce gona da iri a alkaluman da suke bayarwa dangane da halin matsi da al’ummar yankin arewa maso gabashin kasar ke ciki.

Yara a sansanin 'yan gudun hijra dake Maiduguri a jahar Borno.
Yara a sansanin 'yan gudun hijra dake Maiduguri a jahar Borno. OCHA/Jaspreet Kindra
Talla

Sanarwar da mai magana da yawun shugaban kasar Garba Shehu ya fitar a jiyar lahadi, ta bayyana cewa Mjalisar Dinkin Duniya da kuma sauran kungiyoyin na furta irin wadannan kalamai ne domin samun kudaden tallafi daga waje.

A cikin makon jiya ne ofishin kula da ayyukan jinkai na Majalisar Dinkin Duniya ya ce ana bukatar samar da dala milyan dubu daya domin taimaka wa mutane sama da milyan biyar a cikin shekara mai kamawa a yankin wanda ya yi fama da ayyukan Boko Haram.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.