Isa ga babban shafi
Kudancin Afrika

Kungiyoyin agaji na bukatar $1.2 billion domin yaki da fari a Afrika

Kungiyoyin agaji na Duniya sun ce suna bukatar kudi sama da dala biliyan daya don taimakawa wasu kasashen kudancin Afrika shida dake fama da matsalar fari.

Akalla mutane miliyan 12 ke fuskantar barazanar yunwa a kudancin Afrika
Akalla mutane miliyan 12 ke fuskantar barazanar yunwa a kudancin Afrika AFP/Vincent Defait
Talla

Kasashen da fari ya shafa sun hada da Angola da Lesotho da Madagascar sai malawi da Mozambique da Swaziland da Zimbabwe inda akalla mutane miliyan 12 ke fuskantar barazanar yunwa ganin babu sauran abincin balle tsaf-tatacen ruwan sha da zasu yi dogaro nan gaba.

Hukumar ayyukan agajin gaggawa ta Majalisar Dinkin Duniya ko OCHA ta yi gargadin munin al’amarin inda tace in har kungiyoyin basu samu tallafin ba to fa akwai yiyuwar al’ummar wadannan kasashen zasu ta’azzara sakamakon matsanancin yunwa .

Tasirin da igiyar ruwa ta El nino mai karfin gaske ya haifar da matsananciyar yunwa a wadannan kasashen ya kasance mafi muni a tsawon shekaru 35.

Akalla kungiyoyin na bukatar tallafin dala biliyan daya da miliyan biyu don tunkarar wannan matsalar da ta kunno kai dake kuma yiwa rayuwar al’umma sama da miliyan goma barazana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.