Isa ga babban shafi
MDD

MDD ta bukaci kasashen duniya da su fito da hanyoyin magance fari

Hukumar hasashen yanayi ta duniya, ta bukaci gwamnatoci da kuma kungiyoyi masu zaman kansu da su samar da sabbin hanyoyi domin tunkarar yadda fari ke yi wa ayyukan noma barazana a sassa daban-daban na duniya.

Wani manomi yana tafiya saman kunye a yankin Shandong
Wani manomi yana tafiya saman kunye a yankin Shandong Reuters
Talla

Ambaliya da mahaukaciyar guguwa, abubuwa ne da ke shudewa bayan ‘yan sa’o’I ko kuma kwanaki kadan, to amma fari abu ne da illolinsa ke share tsawon watanni ko kuma dogon lokaci kafin shudewarsu a cewar Robert Stefanski wanda shi ne shugaban sashen bunkasa ayyukan noma a hukumar Hasashen Yanayi ta duniya wato DMO.

A cikin shekarun baya-bayan nan dai an samun yawaitar afkuwar fari a kasashe daban daban da suka hada da yankin kusurwar Afirka da yankin Sahel da China da India da Mexico da Brazil da Rasha da Amurka har ma da wasu kasashe na Gabashin Turai.

Duk da cewa wannan matsala ce da ke shafar milyoyin manoma da kuma haddasa hasarar dukiya mai tarin yawa, to amma hukumar mai hasashen yanayi na ganin cewa gwamnatoci da kungiyoyi masu zaman kansu ba sa daukar matakan da suka dace domin tunkarar wannan matsala.

Yanzu haka dai hukumar da sauran hukumomi na Majalisar Dinkin Duniya da ke da ruwa da tsaki a batutuwan da suka shafi ayyukan noma, na shirin gudanar da taro a makon gobe a birnin Geneva, domin samar da sabbin matakan rage kaifin wannan illa ga ayyukan noma a duniya.

Samakon fari da ake samu akai-akai, masana sun ce kusan kodayaushe ana samun hauhawar farashin kayayyakin abinci ne a duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.