Isa ga babban shafi

Najeriya za ta karbi jiragen yaki 24 daga Italiya

Gwamnatin Najeriya na shirin karban wasu jiragen yaki 24 daga kamfanin kere-kere ta Leonardo da ke ƙasar Italiya.

Jiragen yaki
Jiragen yaki AFP - PRAKASH SINGH
Talla

Kakakin rundunar sojin saman ƙasar Air Vice Marshal Edward Gabkwet ne ya sanar da haka a ranar juma’an da ta gabata.

Cikin snarwar da Gabkwet ya fitar, ya ce a na sa ran karban jiragen yakin kirar M-346 a cikin mayawa hudu, kuma kafin karshen shekarar 2024 dinnan kashin farko da adadi 6 na jiragen za su isa Najeriya.

Sanarwar na zuwa ne bayan ziyarar da Mataimakin Shugaban kamfanin na Leonardo, Claudio Sabatino ya kai wa babban hafsan sojin saman Najeriya a ranar laraba, inda ya ce Kamfanin Leonardo zai shafe tsawon shekaru 25 yana kula da jiragen kamar yadda bangarorin 2 suka yarje.

Wannan na daga cikin matakan da gwamnatin Najeriya ke dauka wajen yaki da matsalolin garkuwa da mutane baya ga ayyukan ta’addanci musamman na rikicin boko haram da ya shafi yankin arewa maso gabashin ƙasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.