Isa ga babban shafi

Sojin saman Najeriya sun yi luguden wuta a sansanonin 'yan ta'adda 3 a Zamfara

Runudunar Sojin saman Najeriya ta ce jiragen yakinta sun yi luguden wuta a sansanoni uku na 'yan ta'adda a jihar Zamfara da ke arewacin kasar, inda suka kashe da dama daga cikinsu tare da lalata maboyarsu.

Jirgin yakin Najeriya.
Jirgin yakin Najeriya. © Daily Trust
Talla

Mai Magana da yawun rundunar sojin saman AVM Edward Gabkwet, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Abuja a Alhamis din nan.

Ya kara da cewa dakarunsu na rundunar Operation Hadarin Daji ne suka aiwatar da wannan gagarumin aiki, wanda suka samu nasarar hallaka da dama daga cikin ‘yan ta’addan.

A cewar Gabkwet sansanonin da aka yi wa luguden wuta na fitattun yan ta'adda ne da suka hadar da sansanin Abdullahi Nasanda da ke Zurmi.

Sai sansanin Malam Tukur da ke Gusau da kuma wani sansani a karamar hukumar Maradun dukkan su a jihar ta Zamfara.

Jihar Zamfara dai na daga cikin jihohin da ke fama da matsalar 'yan bingida a shiyar Arewa maso Yammacin Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.