Isa ga babban shafi
Najeriya

Najeriya na bin NNPC bashin tiriliyan 4.9

Hukumar tarawa da kuma raba arzikn kasa ta Najeriya, RMAFC ta ce, adadin kudaden da kamfanin mai na NNPC ya ki saka wa a asusun gwamnatin tarayya, ya kai Naira tiriliyan 4 da biliyan 900.

Ginin Kamfanin NNPC a Najeriya
Ginin Kamfanin NNPC a Najeriya RFI
Talla

A cikin sanarwar da hukumar ta fitar, mai magana da yawunta, Ibrahim Mohammed ya ce, alkaluman da ke hannunsu, sun nuna cewa gwamnatin Najeriya na bin NNPC wadannan kudaden ne daga watan Janairun shekarar 2011 zuwa Disambabn bara.

Wannan dai na zuwa ne ‘yan kwanaki kalilan da babban mai binciken kudaden gwamnatin kasar, Samuel Ukura ya bayyana cewa, NNPC ya ki sanya Naira tiriliyan 3 da biliyan 235 a cikin asusun gwamanti a shekara ta 2014.

To sai dai kamfanin ya musanta rahoton Mr. Ukuru, inda ya ce, adadin abinda ake bin sa bai wuce Naira biliyan 326 da miliyan 14 ba.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.