Isa ga babban shafi
Najeriya

Ma'aikatan NNPC na Najeriya sun janye yajin aiki

Ma’aikatan kamfanin mai na NNPC a Najeriya sun janye yajin aikin da suka shiga sakamakon matakin da gwamnatin kasar ta dauka na karkasa kamfanin gida 7.

Karamin ministan man fetir a Najeriya, Emmanuel Ibe Kachikwu.
Karamin ministan man fetir a Najeriya, Emmanuel Ibe Kachikwu. AFP PHOTO / STRINGER
Talla

Rahotanni sun ce kungiyoyin gwadago na ma’aikatan sun aike da sakon kar ta kwana ga mambobinsu da ke fadin kasar, inda suka umarce su da su koma bakin aiki.

Wannan na zuwa ne bayan ministan mai na kasar, Emmanuel Ibe Kachikwu ya gana da kungiyoyin a yau Alhamis a birnin tarayya Abuja.

A farko dai ma’aikatan sun koka kan yadda gwamnatin kasar ta yi gaban kanta wajen daukan matakin karkasa kamfanin ba tare da ta tuntube su ba, lamarin da ya tinzira su har suka tsindima cikin yajin aikin.

Gwamnatin dai ta ce ta dauki wannan matakin ne domin samar da sabbin sauye sauye a kamfanin na NNPC da nufin magance matsalar cin hanci da rahawa.

A hirarsa da rfi hausa, Alhaji Umar Dembo, tsohon ministan albarkatun mai a Najeriya ya ce, ya kamata a tuntubi ma’aikatan kafin gwamnati ta dauki wannan matakin na karkasa kamfanin.

Ga dai cikakkiyar hirarsa da Bashir Ibrahim Idris.

03:31

Alhaji Umar Dembo kan karkasa NNPC a Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.