Isa ga babban shafi
Najeriya

Za a gurfanar da masu almubazzaranci a NNPC-Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buahari ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba, za a gurfanar da wadanda suka yi almubazzaranci da biliyoyin kuadade mallakan Kamfanin mai na Kasar, NNPC. 

shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
shugaban Najeriya Muhammadu Buhari RFI Hausa
Talla

Buhari ya fadi haka ne a ganawar da ya yi da shugaabn Kasar China Xi Jinping a jiya lahadi a birnin New York na kasar Amurka.

Buhari ya kara da cewa gwamantinsa a shirye take domin tabbatar da tsafta a Kamfanin NNPC ta yadda zai kubuta daga matsalar cin hanci da rashawa.

To sai dai shugaban na Najeriya bai sanar da lokacin da za a gurfanar da wadanda ake zarigi da almubazzaranci da kudaden ba.

,
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.