Isa ga babban shafi
Najeriya

Saraki zai bayyana a gaban Kotu a yau

Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Bukola Saraki ya ce yau zai gurfana a gaban kotun ladabtar da ma’aikata wadda ta bada sammacin kamo shi a karo na biyu.  

Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Bukola Saraki
Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Bukola Saraki REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Kotun ta bukaci Saraki ya bayyana a gabanta sakamakon tuhume tuhume 13 da ake masa na bada bayanan karya a lokacin da yake Gwmanan jihar Kwara.

Tuni dai Kotun ta bukaci Babban Speto Janar na Yan Sandan Najeriya, da ya kamo mata Saraki a duk inda yake matukar ya ki bayyana a gabanta a yau latata.

To sai dai lauyan dake kare shugaban Majalisar Dattawan Joseph Daudu, ya shaidawa RFI hausa cewa, zasu mutunta doka duk da dai kotun ba ta gamsu da jawaban da suka gabatar mata ba a farko.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.