Buhari ya wanke kan sa a tuhumar Saraki
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nesanta kan sa daga zargin da ake masa na hannu wajen tuhumar da ake yiwa shugaban Majalisar Dattawan kasar Bukola Saraki a gaban kotu.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Wata sanarwar da mai Magana da yawun shugaban Garba Shehu ya fitar na cewa Buhari ba shi da hannu cikin shari’ar, kuma a matsayin sa na wanda ya yi rantsuwar kare kundin tsarin mulkin kasa babu yadda zai sa baki kan harkokin shari’a.
Magoya bayan shugaban Majalisar na zargin cewa da hannun gwamnati a tuhumar da ake yiwa saraki yanzu haka.
A na zargin Saraki da aikata laifuka 13 dangane da bada bayanan karya kan kadarorin da ya mallaka.
A ranar jumma’ar da ta gabata ne Kotun ladabtar da ma’aikata a Najeriya ta ba da sammacin kama shi bayan ya ki halartar kotun domin fuskantar shari’a.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu