Isa ga babban shafi

Kasashen Duniya na fatan kawo karshen yaduwar makamin Nukiliya

Manyan kasashen duniya biyar da ke da karfin makamin Nukiliya sun sha alwashin shawo kan yadda makamin, mai matukar hadari ke yaduwa tsakanin kasashen duniya.

Tutar kasar Iran a harabar hukumar sa ido kan makaman nukiliya
Tutar kasar Iran a harabar hukumar sa ido kan makaman nukiliya REUTERS - Leonhard Foeger
Talla

Masana harkokin tsaro da alakar kasashe na ganin cewa kasashen na fargabar abinda kaje ya zo game da zaman lafiyar duniya da kan iya shafar su, shine ma dalilin da ya sa suka dauki wannan mataki.

Wannan na zuwa ne kafin taron sake nazartar yarjejeniyar mallakar makamin a kasashen suka rattabawa hannu da ake yi duk shekara.

Taron manyan kasashen duniya a kan kasar Iran
Taron manyan kasashen duniya a kan kasar Iran Handout EU DELEGATION IN VIENNA/AFP/File

Taron da kuma sake nazartar dokar da aka saba gudanarwa duk ranar 4 ga watan Janairu na cikin tanade-tanaden dokar mallakar makamin wadda aka samar tun shekarar 1970, don kare duniya daga irin bannar da wadannan makamai ka iya yi mata, wanda shine ma dalilin da ya sa ake takaita kasashen da zasu iya mallakar sa.Tuni dai kasashen duniya irin su China da Russia da Faransa suka goyi bayan hakan, suna masu ganin cewa hakan wata hanya ce ta tabbatar da zaman lafiyar duniya da kuma karfafa kyakyawar alaka da yarda da juna tsakanin kasashen duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.