Isa ga babban shafi
iran - tsaro

Wasu karin 'yan sandan Iran uku sun mutu cikin makon da ya gabata

An kashe karin 'yan sandan Iran uku cikin wannan mako, lamarin da ya haura adadin jami'an da suka rasa rayukansu zuwa shida a wani tashin hankalin da aka samu a kasar.

'Yan sandan kwantar da tarzomar Iran watan Yuli shekarar 2009
'Yan sandan kwantar da tarzomar Iran watan Yuli shekarar 2009 STR/AFP/File
Talla

A ranar Juma'a, an kashe wani kyaftin a lardin Khuzestan da ke kudu maso yammacin kasar yayin wani samame da aka kai kan "sansanin 'yan fashi da makami", in ji kamfanin dillancin labarai na Tasnim.

A cewr majiyar, kwana guda kafin haka, wani dan sanda ya mutu sakamakon raunukan da ya samu yayin arangama da ‘yan daba masu dauke da makamai a lardin Isfahan da ke tsakiyar kasar, baya ga wani dan sandan da motar dakon mai ta taka ranar Laraba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.