Isa ga babban shafi
Girka

Majalisar Girka ta amince da dokar zaftare guraban ayyuka 15,000

Majalisar Kasar Girka ta amince da wata sabuwar dokar aikin Gwamnati, wadda za ta sa ma’aikata 15,000 su rasa ayyukan su a shekara mai zuwa. Ita dokar wadda ta kawo karshen zama akan gurabun ayyuka har sai mutum ya mutu, ta samu amincewar ‘Yan Majalisu 168, yayin da 123 suka ki amincewa da ita.  

Majalisar Dokokin kasar Girka
Majalisar Dokokin kasar Girka 路透社
Talla

Ana saran maye guraban aiyukan da matasa wadanda basu da aiyukan yi.

Wanna doka itace ier iren tsare tsare da gwamnatin ta Girka ke yi na tsuke bakin aljihu domin farfado da tattalin arzikin kasar, wanda ke fama da matsaloli iri iri.

Tun a shekarar 1911 ne kasar tag Girka ta fitar da wata doka da ta bawa ma’aikata damar zama akan guraban ayyukansu har iya zuwa tsawon rayuwarsu a matsayin kariya koda an samu canjin gwamnati.

A yanzu haka ana san ran dokar za ta fara aiki daga matakin Jihohi kamin ta kai ga matakin kasa baki daya.

Sai dai kungiyoyin kwadago daban daban sun nuna rashin amincewarsu da wannan doka inda suka yi kira da a fito gudanar da zanga zanga a kofar dakin majalisar kasar.
Tuni hukumomi a kasar suka jibge jami’an tsaro a kofar shiga majalisar tun a ranar Lahadi domin kare lafiyar ‘Yan majalisun.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.