Jamus na zawarcin ma’aikata daga kasashen dake fama da matsalar tattalin arziki
Ma’aikatar kula da diban ma'aikata a kasar Jamus ta fara gayyatar likitoci da kuma masana harkar kimiyya zuwa kasarta, daga kasashen Gabashin Nahiyar Turai da ke fama da matsalar tattalin arziki. Jamus ta kasance kasa a Nahiyar ta turai da ta fi kowace kasa yawan arziki.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
‘‘Kasar Jamus za ta tarbi ma’aikata a fannoni daban-daban da yawansu ya kai 200,000 a duk shekara domin magance matsalar rashin ma’aikata a kasar’’ Inji shugaban dake kula da ma’aikatar diban ma’iakata, Frank- Juergen.
Yawan ma’aikata da kasar ta Jamus ta diba daga kasashen Girka da Italiya da kuma Spain ya haura da kashi takwas a shekarar da ta gabata, a cewar Juergen.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu