Hada - hadar kasuwancin Jamus ya bunkasa bayan karuwar fitar da kayayyaki daga kasar
Hadahadar kasuwanci ya bunkasa a kasar Jamus bayan karuwar fitar da kayyaki kasar zuwa kasashen waje domin kasuwanci, a yayin da shiga da kayyaki cikin kasar ma ya karu tun a watan Janairun wannan shekara. Kasar ta Jamus, wacce ita ce kasa da ta fi karfin tattalin azriki a Nahiyar Turai, na fitar da kayyayakinta zuwa kasashen waje da yawan kudinsu ya kai kudin Euro biliyan 19.9 a shekara, a cewar hukumar yin kididdiga a kasar.
Wallafawa ranar:
Hakan kuma ya dare kiyasin da masana suka yi na karuwar hadahadar kasuwanci da kashi 0.5, inda fitar da kayyayakin kasar ya auku cikin gaggawa inda aka samu kari daga 3.3 zuwa kudi biliyan 76.2 na kudin Euro.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu