Isa ga babban shafi
Girka

Rashin aikin yi ya karu da kashi 26 a Girka

Rashin aikin yi ya karu da kashi 26 a watannin karshen shekarar 2012 a kasar Girka inda aka hada da kwatankwacin shekarar 2011 inda rashin aiki ya karu da kashi 20.7 a kasar. Rashin aikin yi ya karu da kashi 24.8 a tsakiyar shekarar ta 2012 kamar yadda wata rubutacciyar sanarwa da ta fito daga Hukumar kididdiga ta kasar ta bayyana.  

'Yan kasar Girka na nuna rashin jin dadinsu akan matakan tsuke bakin aljihu da gwamnatin Girka ta yi
'Yan kasar Girka na nuna rashin jin dadinsu akan matakan tsuke bakin aljihu da gwamnatin Girka ta yi REUTERS/John Kolesidis/Files
Talla

Yawan marasa aikin yi a Girka a watanni uku karshe na shekarar ta 2012 ya kai har yawan mutum sama da miliyan daya, yayin da mutum sama da miliyan uku ne ke aiki a kasar.

Bayanana da suka fito sun kuma nuna cewa mata sun fi yawan rashin aikin yi da kshi 29.7 idan aka kwatanta da maza da suke da kashi 23.3 a matsalar rashin aikin yi.

Domin ganin ta ceto kasar daga matsalar tabarbarewar tattalin arziki, gwamnatin Girka ta dauki matakan tsuke bakin aljihu wanda hakan ya taimaka mata wajen samun tallafi daga kasashen duniya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.