Isa ga babban shafi
Najeriya,Girka

Burtaniya da Italiya da Girka sun tabbatar da kisan Turawan da Ansaru ta yi garkuwa da su

Kasashen Britaniya, da Italya da Girka sun ce akwai kamshin gaskiya kan ikirarin da kungiyar nan ta Ansaru ta yi, na hallaka ‘yan kasashen su 7, da take garkuwa da su a arewacin Nigeria. An dai kama wadannan ‘yan kasashen wajen ne a jihar Bauchi, kuma bayannai sun nuna cewar ma’aikatan wani kamfanin gine-gine ne dake aikin gini a yankin na Arewa maso yammacin tarayyar Najeriya.

Capture d'image d'une vidéo diffusée par le groupe islamiste Ansaru le 24 décembre 2012
Capture d'image d'une vidéo diffusée par le groupe islamiste Ansaru le 24 décembre 2012 AFP PHOTO - JAMA'TU ANSARUL MUSLIMINA FI BILADIS SUDAN
Talla

A watan da ya gabata ne rundunar ‘yan sandan Nigeria ta ce mutanen da aka yi garkuwar da su sun hada da ‘yan kasar Lebanon 4, sai ‘yan kasashen `Britaniya da Girka da Italiya da dai sauran su.

Kasashen Britaniya, Italya da Girka daka sun yi Allah-wadai da lamarin, inda suka ce kisan gilla ne, da aka yi babu gaira babu dalili. A ranar Asabar da ta gabata ne kungiyar ta bayar da sanarwar mutuwar dukkan mutanen 7, da suka kame a garin Bauchi da ke arewacin Nigera, lokacin da suke aiki da wani kamfani mai suna Setraco.

Kungiyar ta Ansaru, ta kuma nuna wasu hotuna, da tace gawawwakin mutanen da ta yi garkuwa da su ne, inda tace nan gaba za ta fidda hotunan Bidiyo, kan wannan ikirarin nata.

Cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar tace yunkurin da hukumomin Britaniya da na Nigeria suka yi, na ceto mutanen daga wurin su ne, ya sa ta dauki wannan matakin.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.