Isa ga babban shafi
Najeriya

Kungiyar Ansaru ta kashe ‘yan kasashen waje 7 da ta yi garkuwa da su a Najeriya

Wannan kungiyar da ke kiran kanta da Suna Ansaru, tace ta dauki matakin kisan ‘yan kasashen wajen nan da take rike dasu ne sakamakon yunkurin da kasashen Najeriya da Burtaniya ke yin a kubutar da su daga Hannun su

Gawar Hoton Bidiyo na 'yan kasashen waje da Ansaru ke garkuwa da su
Gawar Hoton Bidiyo na 'yan kasashen waje da Ansaru ke garkuwa da su
Talla

Sai dai har yanzu ba’a samu tabbacin labarin daga bangaren gwamnatin tarayyar Najeriya ba kan wannan kisan da kuma kasashen da wadanda akayi garkuwar dasu suka fito.

Jami’an kamfanin Gine-gine da ake kira Setraco sun shaidawa kamfanin dillancin Labarai na AFP cewar suna sane da labarin amma kuma ba zasu iya tabbatar da shi ba.

A wata Takardar bayani da kungiyar ta fitar ta bayyana cewar mambobinta sun kashe daukacin ‘yan kasashen wajen da suke rike dasu.

Jami’an ‘yan sanda a tarayyar Najeriya dai sun bayyana wadanda akayi garkuwa dasu a matsayin ‘yan kasashe daban-daban da suka hada da Lebanon da Burtaniya da Girka da Italiya, koda yake akwai wasu bayannai dake nuna cewar akwai dan kasar Siriya a ciki.

An dai kama wadanda ake garkuwa dasu din ne a ran 16 ga watan Fabrairu a jihar Bauchi dake Arewacin kasar.

A wani labarin kuma jami'an Soji a Najeriyar sun bayyana kisan 'ya'yan kungiyar Boko Haram 20 a wani dauki-ba-dadi da sukayi da su a Maiduguri

Wannan dai na zuwa ne sa'o'i kalilan da shugaban kasar Goodluck Jonathan ya kammala ziyarar kwana 2 a yankin na Arewa maso yammacin Najeriya.

Sojin haka ma a ranar Jumu'a sun bayyana cewar sun dirar wa wani Kauye ne da ake zaton nan ne mafakar 'yan Boko Haram inda suka kama akalla mutum 25.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.