Isa ga babban shafi
Najeriya

'Yan sandan Jihar Bauchi sun tabbatar akwai dan Birtaniya cikin wadanda aka yi garkuwa da su

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Bauchi, ta yi karin haske kan ma’aikatan da aka kama a Jama’are, inda ta ce ‘yan bindigar sun fara kai hari ne kan ofishin ‘yan sanda kamin kai hari a ma’aikatar da suka kama mutane bakwai. Mai magana da yawun 'yan sandan, ASP Mohammed Hassan Auyo, ya ce 'yan bindigan sun fara kai hari ne a ofishin 'yan sanda da gidan yari. 

Shugaban 'Yan sandan Najeriya, Mohammed Dahiru Abubakar.
Shugaban 'Yan sandan Najeriya, Mohammed Dahiru Abubakar.
Talla

“Gudun da suka yi bayan an korarsu daga ofishin ‘yan sanda da gidan yari, sai ‘yan bindigan suka bi ta wani kamfani da ake kira SETRACO a Jama’are, suka shiga suka kashe daya daga cikin masu gadin kamfanin suka kuma kama ma’aikata turawa da suke aiki a wurin.” Inji ASP Hassan.

Ya kara da cewa “hudu daga cikin mutanen da aka yi garkuwan da su hudu Lebanese ne, daya dan kasar Birtaniya ne, daya dan kasar Girka ne da kuma wani dan kasar Italiya guda daya, wanda ya kawo jumulalrsu zuwa mutum bakwai.”

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.