Isa ga babban shafi
Najeriya

'Yan bindiga sun yi garkuwa da wasu ‘yan kasashen waje a Najeriya

Rahotanni daga Najeriya na nuna cewa wasu ‘Yan bindiga suna garkuwa da wasu ma’aikata su bakwai ‘yan kasar waje wanda ke aiki a wani kamfani dake garin Bauchi mallakar wani dan kasar Lebanon, cikinsu har da wani dan kasar Girka. A yayin yin garkuwa da mutanen, daya daga cikin masu tsaron kamfanin ya rasa ransa.  

Garin Bauchi dake Tarayyar Najeriya
Garin Bauchi dake Tarayyar Najeriya AFP/Tony Karumba/File
Talla

Ofishin jakadancin kasar Girka dake Najeriya ya tabbatar da aukuwar wannan lamarin inda bayyana yin garkuwan da daya daga cikin ‘yan kasarsa.

Kamfanin wanda akewa lakabi da SETRACO yana karamar hukumar Jama’are ne a Jihar ta Bauchi, a yayin da tuni ofishin jakadancin kasar ta Girka ya sanar da iyalan dan Girkan da ake garkuwa da shi.
 

Wasu daga cikin ‘yan kasashen wajen da ake garkuwan da su, sun hada da wani dan kasar Italiya da kuma dan kasar ta Lebanon.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.