Isa ga babban shafi
Faransa-Mali-Najeriya

Hollande da Goodluck sun gana game da rikicin Mali

Shugaba Francois Hollande ya ce Dakarun Faransa suna zangon karshe na yankunan da ke karkashin ikon ‘Yan tawayen Mali amma Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, yace duk da ya ke an samu nasarar kwace manyan garuruwan Arewaci da ‘Yan tawaye suka kwace, har yanzu akwai sauran aiki a gaba.

Shugaban Faransa Francois Hollande (dama) da Shugaban Najeriya Goodluck Ebele Jonathan suna ganawa da manema labarai a fadar Elysee a birnin  Paris
Shugaban Faransa Francois Hollande (dama) da Shugaban Najeriya Goodluck Ebele Jonathan suna ganawa da manema labarai a fadar Elysee a birnin Paris REUTERS/Philippe Wojazer
Talla

Shugaba Hollande yace dakarun Faransa sun samu nasarar kwace mafi girman farfajiyar Yankin Arewaci Mali sai dai ya yi gargadin akwai barazanar hare haren kunar bakin wake daga masu kishin Islama.

Bayan ganawa da shugaban kasar Faransa, francois Hollande a birnin Paris, Shugaba Jonathan na Najeriya ya shaidawa RFI cewa ba a samun nasara kan ‘yan ta’adda cikin kankanin lokaci ba domin suna narkewa ne a cikin jama’a su dinga kai hare hare kamar yadda yak e faruwa a Najeriya.

A ranar 11 ga watan Janairu ne Faransa ta kaddamar da yaki a Mali bayan aikawa da dakarunta kimanin 4,000 da kuma jiragen yaki. Amma sun yi nasarar kwato manyan biranen Arewaci Gao da Timbuktu da Kidal da suka fada ikon ‘Yan tawaye tsawon watanni 10.

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan yace matsalar ta wuce kakkabe ‘Yan tawaye illa a yi kokarin girke tsaro a kasar.

A wata Sanarwa a shafin Intanet, Kungiyar Al Qaeda a reshen Yemen ta yi kiran kaddamar da jihadi domin karya dakarun Faransa a Mali. Suna masu cewa yaki da Musulmi ya shafi musulmi.

Gwamnatin Amurka ta yi alkawalin bayar da tallafin kudi Dala Miliyan 50 ga dakarun Faransa da Chadi wadanda suka shiga tsakanin rikicin kasar Mali.

Tun da farko kasar Amurka ce ta dauki nauyin jigilar dakarun Faransa da Chadi zuwa kasar Mali domin yaki da ta’addaci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.