Isa ga babban shafi
Faransa

Ana zargi rakumin da aka bawa Hollande kyauta a Mali sato shi aka yi

Rahotannin na nuna cewa yanzu ta tabbata cewa sato rakumi aka yi aka baiwa Shugaban kasar Faransa kyauta saboda jagorantar koran ‘Yan tawaye daga Arewacin kasar Mali. A ranar Asabar data gabata ne dai, yayin wata ziyarar bazata, da Shugaban Faransa Francois Hollande ya kai garin Timbuktu na kasar Mali, aka yi ta jinjina masa, da har akayi masa kyautan karamin rakumin saboda jagorantar da Faransa ta yi na koran ‘Yan tawaye daga Arewacin kasar Mali.  

Lokacin da daruruwan mutane suke tarban Francois Hollande a Mali a yayin ziyarar tasa
Lokacin da daruruwan mutane suke tarban Francois Hollande a Mali a yayin ziyarar tasa Reuters/Joe Penney
Talla

Anyi ta nuna hoton rakumin da kuma shi Shugaban Faransan, yana murna saboda wannan kyauta, inda har shugaban Faransa ya rika lallashin rakumin dake gurnani.

Bayanai yanzu na nuna cewa ashe sato wannan rakumi akayi daga wani manomi, wanda akayi wa fin-karfi, da lalata masa gidansa da Dakarun Faransa suka yi.

Bayanai na cewa wanda ya mallaki rakumin da aka yi kyautan dashi, yanzu haka yana zaune ne a wani sansanin ‘yan gudun hijira dake Ambra, dab da kan iyakan Mali da Mauritania.

Mai wannan rakumi da ya ce sunansa Said, ya yi barazanar kai batun gaban kotu.

Babu dai wasu bayanai daga fadar Shugaban kasar Faransa har ya zuwa wannan lokaci.

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.