Isa ga babban shafi
Mali-Faransa-Chadi

Dakarun Faransa da Chadi, na ci gaba da kutsa kai mafakar 'Yan tawayen Mali

Harin da dakarun kasar Faransa ke yi a Mali, mai lakabin operation Serval, wanda ke nufin sunan wata dabbar Hamada, an kaddamar da shi ne makwanni 4 da suka gabata.

Dakarun sojan Faransa a kewayen filin jirgin saman Bamako ranar  23 janwaren 2013.
Dakarun sojan Faransa a kewayen filin jirgin saman Bamako ranar 23 janwaren 2013. REUTERS/Malin Palm
Talla

Manufar kai hari dai shine, kokarin taka birki ga ci gaba da dannawar da dakarun kungiyoyin masu kishin Islama da suka mamaye yankin arewacin kasar ta Mali yau da kimanin watanni 9 da suka gabata ke yi.

Yanzu haka dai, mafi girman fadin kasar ta Mali ya samu kubuta daga yan tawaye, inda kuma dakarun Fransa da Tchadi ke ci gaba da fatatakar kungiyoyin mayakan jahadi da suka watsu, musaman a tsaunukan Ifoghas.

A jiya alhamis Dakarun Faransa da Tchadi sun isa a garin Aguelhok, mai tazarar kilo mita 160 da birnin Kidal, Aguelhok dai nan ne mayakan masu tsananin kishin islama suka warwatsu a tsaunukan dake arewa maso gabashin kasar, sai dai kuma kawo yanzu babu labarin barkewar fada .

Daga wannan yanki mai tsaunuka na Aguelhok ne, dakarun Faransa da Tchadi da suka baro sansanoninsu na Kidal, zasu zarce zuwa garin Tessalit, mai tazarar kilo mita 100 Aguelhok, domin kwato shi daga hannun mayakan na yan tawaye, saboda muhimmancin da garin yake da shi, sakamakon kasancewarsa da babban filin tashi da saukar jiragen sama.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.