Isa ga babban shafi
Faransa

Hollande zai kai ziyara kasar Girka ranar Talata

Shugaban kasar Faransa, Francois Hollande, zai kai wata muhimmiyar ziyara kasar Girka a ranar Talata mai zuwa domin nuna goyon bayan kasarshi ga kasar ta Girka a yayin da Girkan ke fama da matsalar tattalin arziki. 

Shugaban kasar Faransa, Francois Hollande
Shugaban kasar Faransa, Francois Hollande Reuters
Talla

Masu saka ido kan harkokin siyasar duniya sun yi hasashen cewa wannan ziyara zata karfafawa kasar ta Girka kwarin gwiwa, inda ya dade yana fafutukar ganin cewa kasar bata fice daga yankin kasashen dake amfani da kudin Euro ba.

A watan Disambar shekarar da ta gabata ne Shugabannin Kungiyar nahiyar ta Turai suka yi alkawarin bawa kasar ta Girka tallafin Dalar Amurka biliyan 66 idan har ta amince ta dauki matakan tsuke bakin aljihu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.