Isa ga babban shafi
Faransa-India

Shugaba Hollande na Faransa yana ziyara a kasar India

Shugaban Faransa, Francois Hollande, ya fara ziyarar aiki ta kwanaki biyu a kasar India, inda ake sa ran zai farfado da cinikin jiragen saman yaki tsakanin kasashen biyu. Wannan ziyarar, ita ce ta farko da Shugaban ya kai Nahiyar Asia, inda Faransa ke fatar ziyarar za ta taimaka wajen bunkasa harkokin kasuwanci na shekaru 15, da ke tsakanin kasashen biyu.

Shugaban Faransa, François Hollande tare da Prime Ministan  PIndiya, Manmohan Singh
Shugaban Faransa, François Hollande tare da Prime Ministan PIndiya, Manmohan Singh Reuters / Mathur
Talla

A cikin tawagar Shugaba Hollande, akwai Ministoci biyar, cikin su har da Ministan harkokin waje Laurent Fabius, da Ministan tsaro Jean Yves Le Drian da kuma 'Yan kasuwa sama da 60.

Ma’aikatar harkokin wajen India tace dangantakar kasashen biyu na ci gaba da karuwa a fannonin kasuwanci, tattalin arziki da kuma masana’antu.

Ana saran shugaba Hollande zai gana da Prime Minista, Manmohan Singh a birnin New Delhi, kafin ya tafi birnin Mumbai don ganawa da ‘yan kasuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.