Isa ga babban shafi
Faransa

Majalisar Dokokin Faransa ta amince da Auren jinsi

Majalisar Dokokin kasar Fransa ta amince da sabuwar dokar hallata auren jinsi a kasar bayan tabka muhawara mai zafi. Wannan ne matakin na farko mai karfi da ‘Yan Jam’iyyar Socialist suka samar tun darewar Francois Hollande kan karagar shugabancin kasar Faransa.

Wasu Mata 'Yan Madigo a bainar Jama'a a birnin Paris.
Wasu Mata 'Yan Madigo a bainar Jama'a a birnin Paris. Carina Branco
Talla

‘Yan majalisar dokokin sun amince da dokar da za maza za su iya auren juna kamar yadda mata ma za su iya auren junansu.

Dokar Auren jinsin ta samu rinjayen kuri’u 329 a kan kuri’u 229 da suka kada kuri’ar kin amincewa da dokar.

Wannan ya zama na farko a jerin sauye sauyen da ‘Yan socialist ke son kawowa tun bayan zaben da ya kai Francois Holland kan kujerar mulkin kasar Fransa.

Firaminsiatan kasar Fransa Jean Marc Ayrault ya ce wannan mataki ne da zai ba Faransa ‘Yancinsu. Ya kuma kara da cewa, dokar na daga cikin jerin dokokin da suke son haifar da sauye sauye ga Jamhuriya wajen samar da daidaito tsakanin al’umma.

Wannan zabe ya kawo karshen mahawarar tsawon kwanaki 10 da Majalisar dokokin kasar ta Fransa ta yi kan Auren jinsi, kafin mikata ga majalisar dattijai domin sake yin nazari a kai a watan gobe.

Tun fara muharar dubban al’ummar kasar Faransa musamman mabiyar darikar Katolika suka fito domin adawa da la’antar dokar halattawa ‘Yan madigo da ‘Yan luwadi auren junansu.

Dubban masu adawa da dokar Auren Jinsin sun shirya gudanar da zanga-zanga a ranar 24 ga watan Maris.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.