Isa ga babban shafi
Faransa

Zanga-zangar Auren jinsi a Faransa

Mabiya darikar Catholica kimanin 100,000 ne suka shiga zanga-zangar lumana a kasar Faransa, don nuna adawarsu da shirin gwamnatin kasar na amincewa da dokar halarta auran jinsi a Faransa, suna masu cewa matakin ya sabawa addini da al’adun Bil Adama.

dubban Mutane da suka fito suna zanga-zangar adawa da hallata auren jinsi a Faransa
dubban Mutane da suka fito suna zanga-zangar adawa da hallata auren jinsi a Faransa REUTERS/Christian Hartmann
Talla

Cikin masu zanga-zangar har da matasa sanye da kayan Coci, inda suke cewa fatar su shi ne kare iyalinsu da ‘yayansu.

Sai dai kuma akwai wasu kungiyoyin mata ‘Yan Madigo da suka gudanar da ta su irin zanga zangar domin neman ba su hakkinsu.

‘Yan madigon sun fito tsirara ba riga dauke da wasu kalaman batanci ga malaman addinin kirista da ke la’antar haramta dokar auren jinsi.

‘Yan sandan Faransa dai sun cafke matasa da dama da suka fito domin karo da ‘Yan Madigon da ke gudanar da Zanga-zanga inda suka harba hayaki mai sa hawaye.
Gwamnatin Hollande dai na fuskantar Suka daga malaman addini a Faransa da kuma ‘Yan adawa.

Fafaroma Benedict ya yi kira ga majami’un Faransa su dage wajen neman ‘Yancinsu.

Sai dai Ministan kula da rayuwar jama’a, Marisoul Touraine, tace tana mutunta bukatun masu zanga zangar, amma kuma gwamnati ba zata sauya matsayin ta ban a amincewa da dokar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.