Isa ga babban shafi
Faransa

Gwamnatin Faransa ta amince da auren jinci

Gwamnatin Jam’iyyar gurguzu ta François Hollande ta amince da yin auren jinsi a kasar Faransa duk da la’antar matakin da Darikar Katolika ta yi da kuma ‘Yan adawa. Tsohon shugaban kasa Nicolas Sarkozy na Jam’iyyar UMP ya nemi a gudanar da muhawara game da batun.

Wasu 'Yan madigo suna sunbatar Juna a bainar Jama'a a kasar Faransa
Wasu 'Yan madigo suna sunbatar Juna a bainar Jama'a a kasar Faransa AFP/Gérard Julien
Talla

Tun a yakin neman zaben shi ne François Hollande ya yi alkawalin bai wa ‘Yan luwadi da ‘Yan Madigo ‘Yancinsu. Shugaban ya shaidawa Ministocinsa cewa amincewa da kudirin wani ci gaba ne a Faransa.

A Watan Janairu ne za’a gabatar da kudirin a Zauren Majalisa wanda kuma zai ba ‘Yan luwadin damar mallakar dan da ba nasu ba.

Sai dai kuma Darikar Katolika ta la’anci kudirin tana mai cewa ya sabawa tsarin rayuwar Dan Adam. Kuma A’lummar Musulmi da Yahudawa suna cikin wadanda ke adawa da kudirin.

Akwai ‘Yan Majalisa da dama da suka bukaci gudanar da zaben jin ra’ayin Jama’a game da wannan batu kafin amincewa da kudirin a kundin tsarin mulkin kasar.

Amma wani ra’ayin jama’a da aka gudanar ya nuna Faransawa kashi 65 sun amince da auren jinsi.

A kasar Amurka, Jahohin Maine da Maryland sun amince da yin auren jinsi bayan gudanar da zaben jin ra’ayin Jama’a.

A Ranar Talata, Kotun kundin tsarin mulkin kasar Spain ta yanke hukuncin amincewa da auren Jinsi.

Kasashen da kuma suka amince da auren jinsi sun hada da kasar Holland da Belgium da Spain da Canada da Afrika Ta Kudu da Norway da kuma kasar Sweden

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.