Isa ga babban shafi
Amurka

Amurka zata yaki haramta auren Jinsi

Gwamnatin Kasar Amurka tace zata yaki kasashen da ke musgunawa ‘Yan luwadi da Madigo, da kasashen da suka dauki matakan hana masu yin auratayya, domin dakile tallafin da take basu.

Taron Jekadun Diflomasiyar wasu kasashen duniya a Geneva lokacin da  Hillary Clinton ke bayyana matakan yaki da haramta auren jinsi
Taron Jekadun Diflomasiyar wasu kasashen duniya a Geneva lokacin da Hillary Clinton ke bayyana matakan yaki da haramta auren jinsi Reuters
Talla

Sakatariyar harkokin wajen kasar, Hillary Clinton ce ta sanar da haka a Geneva, inda take cewa masu auren Jinsi suna da ‘yancinsu kamar yadda, kowane Dan Adam ya ke da nasa ‘yanci.

Wannan mataki na Amurka ya yi dai dai da matakan da Gwamnatin Birtaniya ta dauka, kuma matakan na zuwa ne a dai dai lokacin da gwamnatin Najeriya ta kafa dokar haramta auren Jinsi, matakin da ya janyo kace-nace tsakanin kasashen duniya.

Sai dai a lokacin da Clinton ta gama jawabi nan take ne wasu daga yawancin jekadun kasashen waje suka fice daga dakin da take jawabi.

Matakan hallata Auren Jinsi dai suna daya daga cikin kudirorin gwamnatin Obama kafin sake zabensa wa’adi na biyu a shekarar 2012.

Kasashen Musulmi da dama sun yi watsi da hallata ‘Yancin auren jinsi, musamman kasar Saudiyya da Afghanistan. Sai Clinton tace akwai doka a Amurka da ta tanadi ‘yancin ‘yan luwadi sabanin sauran kasashen da suke la’antar masu wannan tabi’a.

Tun a farkon shekarar nan ne Shugaban kasar Amurka Barack Obama ya amince da dokar Auren Jinsi mai taken ‘kada ka tambaya kada kace komi’.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.