Isa ga babban shafi
Amnesty-Amurka-Tanzania

Kungiyar Amnesty ta bukaci Cafke Bush a ziyararsa kasashen Afrika

Tsohon shugaban kasar Amurka George Bush ya samu tarba ta musamman hannun gwamnatin Tanzania a fara ziyararsa kasashen Afrika duk da kiran da kungiyar kare hakkin Bil’adama ta Amnesty ta yi na Cafke tsohon shugaban.

Tsohon Shugaban kasar Amurka  George Bush  tare da shugaban kasar Tanzania Jakaya Kikwete lokacin da suka kai ziyara ga wata da ta samu tsira daga cutar Cancer Theresia Cosmas Chibongo
Tsohon Shugaban kasar Amurka George Bush tare da shugaban kasar Tanzania Jakaya Kikwete lokacin da suka kai ziyara ga wata da ta samu tsira daga cutar Cancer Theresia Cosmas Chibongo REUTERS/Emmanuel Kwitema
Talla

Bush ya samu tarba ta musamman hannuna shugaban kasar Tanzania Jakaya Kikwete a birnin Dar es Salaam, wanda ya gode wa Amurka ga kokarinta na yaki da cutar Sida ta HIV/AID.

 

A jiya Alhamis ne kungiyar kare hakkin Bil’adama ta Amnesty ta bukaci kasashen Habasha da Tanzania da Zambia cafke George W. Bush bisa zarginsa da keta dokar duniya ta cin zarafin Bila’adama.

Bush ya fara ziyarar ne a kasashen domin inganta hanyoyin yaki da Cutar Sankarar Mahaifa da ta Mama, sai dai kungiyar Amnesty tace kasashen na da hurumin cafke tsohon shugaban karkashin dokar duniya.

Ko a watan Oktoba Amnesty ta bukacin kasar Canada cafke Bush lokacin da ya kai wata ziyara a cikin kasar.

Kungiyar tana zargin Bush ne da cin zarafin Bil’adama tare da ganawa wadanda Amurka ta kama a Guantanamo da Cuba azaba da kuma Afghanistan da Iraqi da dakarun Amurka suka kama.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.