Isa ga babban shafi
Tanzaniya

Mutane 20 sun hallaka sakamakon fashewar makamai a Tanzaniya

Rahotanni daga birnin Dares Salaam na kasar Tanzaniya na cewa mutane akalla 20 sun hallaka sakamakon fashewar nakiya a wata Ma'aikatar makamai na Soja.Bayanan na nuna cewa mutane da dama sun rasa muhallansu. Prime Ministan kasar ta Tanzaniya Mizengo Pinda, ya fadawa Majalisar kasar cewa samada mutane 4,000 dake kusa da barikin sojan suka rasa gidajensu, kuma a yanzu an tsugunar dasu ne a wani filin wasanni yayinda mutane sama da 140 na chan da raunuka.

Tutar kasar Tanzaniya
Tutar kasar Tanzaniya
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.