Isa ga babban shafi
Amurka

Amurka ta aika da jiragen yaki zuwa Korea ta Kudu

Amurka ta aika da jiragen yakinta zuwa korea ta Kudu domin gudanar da atisaye a kudirin kasar na kokarin kare Korea ta Kudu daga barazanar da take fuskanta daga makwabciyarta Korea ta Arewa. Tun lokacin da Korea ta Arewa ta yi nasarar gwajin harba mamakin Nukiliyara karo na uku, danganta ke ci gaba da kazancewa tsakaninta da Korea ta Kudu da kuma Amurka.  

Shugaban kasar Amurka, Barack Obama
Shugaban kasar Amurka, Barack Obama REUTERS/Jonathan Ernst
Talla

Makwanni biyu da suka gabata Korea ta Arewan ta yi barazanar kaiwa Amurka hari saboda goyon baya da ta ke nunawa Korea ta Arewa.

Aikawa da jiragen yakin na Amurka zuwa Korea ta Arewa ya biyo bayan gargadi da Amurkan ta yiwa Korea ta Arewa na ta shiga taitayinta bisa barazanar da kai hare-hare da ta ke yi.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.