Isa ga babban shafi
Korea-Amurka

Korea ta Arewa ta yi barazanar kai hare-hare kan sansanonin Amurka dake Japan

Kasar Korea ta Arewa ta yi barzanar kai hare-hare kan sansanonin kasar Amurka a kasar Japan, a yayin da hankula ke kara tashi game da batun zargin da akewa kasar ta Korea ta Arewa na cewa tana da hanu akan satar bayanai a bankunan Korea ta Kudu.  

Shugaban kasar Korea ta Arewa, Kim Jong -Un
Shugaban kasar Korea ta Arewa, Kim Jong -Un REUTERS/KCNA
Talla

Kasar Korea ta Arewa dai ta yi nasarar gwajin makamai masu linzami na matsakaicin zango, sai dai babu tabbacin ko tana da karfin mallakar makamai masu linzami dake tafiyar dogon zango.

Shugaban kasar ta Korea, Kim Jong – Un ya yi ta barazanar kai hari kan kasar Amurka a ‘yan kwanakin nan, yayin da rahotanni daga Korea ta Kudu ke nuna cewa makwabciyarta na shirin mallakar kuraman jirage masu sarrafa kansu tare da yin amfani da tsofaffin kuraman jiragen da Amurka ta yi wadanda aka shigo da su daga Gabas ta Tsakiya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.