Isa ga babban shafi
Cyprus

Cyprus ta cimma yarjejeniyar samun tallafin kudi biliyan 10 da Tarayyar Turai

Kasar Cyprus ta cimma yarjejeniyar samun tallafin euro biliyan 10 da kungiyar kasahsen Turai, wanda zai kaiga rushewar daya daga cikin manyan bakunan kasar, kana kuma kasar ta cigaba da zama cikin kungiyar kasahsen Turai masu anfani da kudin euro. Wanna ya biyo bayan tattaunawar da shugaban kasar, Nicos Anastasiades ya kwashe sa’oi 12 yana yi da jami’an kungiyar kasahsen Turai tun daren jiya, har zuwa yau da safe.  

Babban bankin Cyprus
Babban bankin Cyprus EUTERS/Bogdan Cristel
Talla

Kwamishinan kudin kungiyar kasahsen Turai, Oli Rehn, ya ce gwamnatiun kasar za ta fara aiki domin tallafawa al’umarta domin farfado da tattalin arzikin kasar.

“Yanzu zamu fara aiki daga yau, dan taimakawa al’ummar kasar Cyprus dan farfado da tattalin arzikin kasar, kungiyar za ta yi iya bakin kokarin ta dan taimakawa jama’a magance matsalar dake iya biyo baya.” Inji Rehn.

Tuni farashin kudin mai ya harba sama a Nahiyar Asiya bayan bawa kasar ta Cyprus tallafi, inda farashin kudin mai mara nauyi ya karu da centi 52 a matsayin kudi Dalar Amurka 94.23 na kowace gangar mai, a yayin da mai nau’in Brent na Arewacin Teku ya karu da centi 62 a mastsayin Dalar Amurka 108.30 a kan kwace gangar mai.

Haka ma a nahiyar ta Turai, kudin Euro ya dawo da karfinsa bayan baiwa kasar ta Cyprus tallafin kudin Euro biliyan 10.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.