Isa ga babban shafi
Cyprus-Rasha-EU

Cyprus tana neman bashi a Rasha

Gwamnatin Cyprus ta nemi bashin kudi a Rasha domin kubuta daga matsalar tattalin arziki da ya addabe ta. Cyprus tana fuskantar barazana daga kungiyar Tarayyar Turai bayan ‘Yan majalisun kasar sun yi watsi da bukatar kasashen Turai.

Bankunan kasar Cyprus
Bankunan kasar Cyprus
Talla

Ministan kudin kasar Michael Sarris ya ce sun cim ma yarjejeniyar da takwaransa na Rasha Anton Siluanov domin karbar bashin.

Ma’aikatar kudin Rasha ta ce Cyprus tana neman bashin kudi euro Biliyan 5 a wata yarjejeniya da suka kulla ta shekaru biyar.

Gwamnatin Cyprus tana neman bashin ne daga Rasha bayan kudirin Tarayyar Turai ya gamu da cika daga ‘Yan Majalisar kasar.

Bankunan kasar Cyprus dai na cikin tsaka mai wuya domin suna iya durkushewa idan har gwamnatin kasar ta kasa samun bashin daga Rasha.

Gwamnatocin kasashen Turai suna fatar gwamnatin Cyprus za ta nemo mafita bayan sun bayyana fargabar kasar na iya ficewa daga euro.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.