Isa ga babban shafi
EU

Taron kasashen Turai zai mayar da hankali akan kasafin kudadensu

Shugabannin Kungiyar kasashen Turai na shirin tafka mahawara kan wani shiri na sanya baki kan kasafin kudin kasashen dake Yankin, dan ganin sun aiwatar da manufofin kungiyar, a taron da za suyi a cikin wanna mako.

Boris Tadic da Herman Van Rompuy  a Hedikwatar kungiyar Tarayyar Turai a Brussels
Boris Tadic da Herman Van Rompuy a Hedikwatar kungiyar Tarayyar Turai a Brussels REUTERS/Francois Lenoir
Talla

Rahotanni sun ce, tuni aka rubuta daftarin yin haka, wanda ake saran shugabanin Faransa ad Jamus za su tattauna akai gobe laraba, kafin taron kungiyar da za’ayi ranar alhamis.

Taron kasashen na zuwa ne a dai dai lokacin da kamfanin Moody da ke sa ido akan darajar bunkuna ya rage darajar bankunan kasar Spain 28 bayan kasar ta bukaci tallafi daga kasashen Turai.

Yanzu haka kuma Kasar Cyprus, ta shiga sahun jerin kasashe biyar, da ke bukatar tallafin kudade daga kungiyar kasashen Turai, don tallafawa bankunan kasar, da ke fama da matsalar basuka. Wannan na zuwa ne bayan hannayen jari sun fadi warwas a kasashen Spain da Italiya da Girka, saboda fargabar Taron kungiyar kasashen Turai da za’a gudanar a ranar Alhamis.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.