Isa ga babban shafi
G20

Kasashen G20 sun yaba da matakan kasashen Turai

Kasashen Turai samu goyon bayan shugabannin kungiyar kasashen G20 a matakan da suke dauka wajen magance matsalar tattalin arzikinsu da ke barazana ga tattalin arzikin duniya.

Shugabannin kasashe 20 masu habakar tattalin arzikin Duniya a taronsu da suka gudanar a kasar Mexico
Shugabannin kasashe 20 masu habakar tattalin arzikin Duniya a taronsu da suka gudanar a kasar Mexico
Talla

Shugaban Kasar Amurka, Barack Obama, yace ya gamsu da shirin shugabanin kasashen Turai, na magance matsalar tattalin arzikin da ya addabi Yankin.

Sanarwar ta fito ne bayan taron shugabanin kasashe 20 da suka fi habakar tattalin arzikin duniya, shugabanin sun ce zasu dauki matakan da suka dace, don kare martabar kudin euro, tare da yaba wa ga shirin kasar Spain na kara yawan kudaden jarin bankunanta.

A nasa bangaren shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin, ya bayyana damuwarsa akan kudin Dalar Amurka, inda yake cewa, yana fargar makomar darajar kudin Dala bayan zaben watan Nuwamba, ganin rabin kudaden ajiyar Rusha kudin Amurka ne.

Putin yace, zai bada shawarar amfani da wasu kuddaden duniya wajen ajiya, maimakon ci gaba da dogaro da Dalar Amurka a taro na gaba da shugaban zai dauki nauyi a Rasha.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.