Isa ga babban shafi
Euro-Spain

Darajar Kudin Euro ya tashi bayan tallafawa bankunan Spain

Darajar Kudin Euro ya tashi da safiyar Litinin bayan da Ministocin kudin kasashen Turai suka bada tallafin kudi euro Biliyan 100 domin ceto bankunan kasar Spain da suka kama hanyar durkushewa.

Tambarin Bankin kasar Spain
Tambarin Bankin kasar Spain REUTERS/Sergio Perez
Talla

An samu tashin Farashin kudin euro a kasashen Asia bayan kasashen Turai sun amince su tallafawa Bankunan kasar Spain.

A birnin Tokyo na kasar Japan kudin euro yana kan gaba akan kudin Dalar Amurka da Kudin Yen.

Wannan tashin farashin na zuwa ne bayan Ministocin kudin kasashen Turai sun amince su tallafawa bankunan Spain da kudi euro Biliyan 100 kusan dalar Amurka Biliyan 125.

Shugaban gwamnatin kasar Spain Mariano Rajoy ya bayyana matukar jin dadinsa dangane da taimakon da kasashen Turai masu amfani da kudin euro suka bai wa bankunan kasar shi.

A ranar Assabar ne kasar Spain ta nemi gudunmuwar kasashen Turai domin tallafawa bankunanta, ba tare da bayyana yawan adadin kudaden da suke bukata ba, kafin kasashen na Turai su bada tallafin na Euro Biliyan 100.

Sai dai yanzu kuma ido ya karkata zuwa ga kasar Italiya da masana tattalin arziki ke tsoron zata kasance mai raunin tattalin arziki a yankin Euro bayan tallafawa kasar Spain.

Hakan kuma ta faru ne bayan wani rahoto da kamfanin Moody mai kididdigar tattalin arziki ya bayyana inda ya ke cewa matsalar kudin da ta shafi bankunan kasar Spain na iya zama tushen matsalar bankunan kasar Italiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.