Shugabannin Turai za su yi kokarin hana Girka ficewa euro
Shugabannin kasashen Turai sun ce za su yi kokarin hana kasar Girka ficewa daga cikin kungiyarsu masu amfani da kudin euro tare da kare matakan tsuke bakin aljihu bayan Shugabannin sun gana a birnin Brussels
Wallafawa ranar:
Wasu manyan jami’an hukumar kungiyar kasashen Turai sun bukaci shugabannin kasashen samar da wani tsari idan Girka ta fice euro.
Bayan kwashe tsawon sa’o’I Shida shugabannin na ganawa a birnin Brussels, sun ce zasu yi kokarin Girka bata fice daga kungiyar euro ba.
“ Muna bukatar Girka a euro, amma muna bukatar kasar ta cim ma bukatun da ta amince da su”. Inji shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel.
Akwai dai sabanin ra’ayi tsakanin Faransa da Jamus tun bayan da Hollande ya gaji Sarkozy a matsayin Shugaban Faransa.
Akwai yiyuwar Girka za ta fice euro idan al’ummar kasar suka kada kuri’ar kin amincewa da tallafin kasashen Turai a ranar 17 ga watan yuni.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu