Yunkurin kafa gwamnatin hadin gwiwa a Girka ya gamu da cikas
Yunkurin kafa gwamnatin hadin gwiwa a kasar Girka ya gamu da cikas bayan Jam’iyyar Syriza ta yi barazanar hada kai da sauran jam’iyyun siyasar kasar. A Yau Litinin ne aka yi hasashen shugaban kasa, Carolos Papoulias, zai jagoanci manyan Jam’iyun kasar uku, don cim ma yarjejeniyar kafa gwamnatin hadin kai.
Wallafawa ranar:
Tun a zaben ranar 6 ga watan Mayu ne masu kada kuri’a suka yi watsi da jam’iyyun da ke goyon bayan matakan tsuke bakin aljihun gwamnati da kungiyar kasashen Turai da hukumar Bada Lamuni ta IMF ke bukata.
Idan dai har Jam’iyyun suka kasa cim ma samar da gwamnatin hadin gwiwa, ya dole a sake gudanar da zabe a watan Yuni.
Sauran Jam’iyyun Siyasar kasar dai suna ganin samar da gwamnati ba tare da samun goyon bayan Jam’iyyar Syriza cikas ne saboda yunkurin samun goyon bayan Majalisa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu