Isa ga babban shafi

Liverpool ta ɓarar da damar komawa jagorancin teburin Firimiya

An tashi wasa canjaras, kwallo 2 da 2 tsakanin Liverpool da Manchester United yayin wasan da ya gudana a Old Trafford wato gidan United, karawar da ke matsayin guda cikin mafiya zafi da kungiyoyin biyu suka yi da juna a baya-bayan nan.

Wasu daga cikin 'yan wasan Liverpool.
Wasu daga cikin 'yan wasan Liverpool. Action Images via Reuters - JASON CAIRNDUFF
Talla

Liverpool din dai ta sha da kyar ne a karawar ta jiya domin kuwa kasa da mintuna 10 kafin tashi daga wasa ne ta iya farke kwallo ta biyu bayan samun bugun fenariti.

Tun farko Liverpool ta zura kwallo ta hannun Luiz Diaz a minti na 23 kuma a haka ne aka tafi hutun tabin lokaci, sai dai kasa da mintuna 5 bayan dawowa daga hutun rabin lokacin ne Manchester United ta farke kwallon ta hannun Bruno Fernandes a minti na 50 ta kuma kara ta biyu ta hannun Mainoo a minti na 67.

Ana 2 da 1 ne tsakanin manyan tawagogin na Ingila biyu ne kwatsam Liverpool ta samu Penalti wanda Mohamed Salah ya yi nasarar zura kwallo.

Duk da yadda Liverpool ta mamaye zagayen farko na wasan, yanayin yadda ta gaza katabus a zagaye na biyu ya bayar da mamaki da kuma sanya fargabar yiwuwar yaran na Jurgen Klopp su bar Old Trafford ba tare da maki ba gabanin bugun fenaritin da ta basu damar tashi wasa 2 da 2.

Dukkanin bangarorin biyu sun yi amfani da zubin ‘yan wasa na 4-3-3.

Wannan canjaras ya dakile Liverpool daga komawa jagorancin a saman teburi bayan da Arsenal ta karbe ragamar a ranar Asabar bayan doke Brighton da kwallaye 3 da nema.

Sai dai har yanzu Liverpool na da maki kankankan ne tsakaninta da Arsenal wato kowacce na da maki 71 in banda banbancin kwallaye, yayin Man City da ke matsayin ta 3 ke da maki 70 bayan da kowannensu ya doka wasanni 31.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.